Amurka-Pakistan

Amurka za ta janye tallafin da ta ke bai wa Pakistan don yakar Taliban

Matakin dai na zuwa ne a dai dai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ke shirye-shiryen kai ziyara don ganawa da sabon Firaministan na Pakistan Imran Khan.
Matakin dai na zuwa ne a dai dai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ke shirye-shiryen kai ziyara don ganawa da sabon Firaministan na Pakistan Imran Khan. PTI handout/via REUTERS

Ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon ta ce ta na shirye-shiryen soke tallafin dala miliyan 300 da ta ke bai wa Pakistan sakamakon gaza katabus wajen kare manufofin Amurkan a kudancin Asiya. Matakin na Amurka dai ka iya zama babbar barazana harkokin tsaron Pakistan.

Talla

Tun a farkon shekarar nan ne Amurkan ta fara barazana kan janye tallafin na dala miliyan 300 don yaki da ta’addanci ga Pakistan, bayan da ta yi ikirarin cewa gwamnatin kasar ba ta da zimmar yakarsu.

Tsawon lokaci Amurkan na Ingiza Pakistan wajen kai hari kan maboyar mayakan Taliban da ke kasar yayinda ta ke tallafa mata da makudan kudade sai dai tana zargin cewa Islamabad bata kai hare-haren kamar yadda ta bukata.

Matukar dai janye tallafin ya tabbata zai zamana kenan Kasar ta Pakistan za ta yi asarar kusan dala biliyan 2 da ta ke samu don yaki da ta’addanci.

Matakin dai na zuwa ne a dai dai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ke shirye-shiryen kai ziyara don ganawa da sabon Firaministan na Pakistan Imran Khan.

A cewar Leitenant Colonel Kone Faulkner na sashen tsaron Amurkan za su ci gaba da matsa lamba ga Pakistan har sai ta amince da yakar kungiyar ta’addancin ta Taliban.

Pakistan dai na ikirarin cewa ta yi asarar dubban rayuka da tarin dunkiya a yakin da Taliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.