Amurka

Shugaba Trump na barazanar cire Canada daga cikin Alena

Tutocin kasashen kungiyar Alena,Mexico,Canada da Amurka
Tutocin kasashen kungiyar Alena,Mexico,Canada da Amurka Nicoguaro/wikimedia.org

Shugaban Amurka Donald Trump a jiya asabar ya yi barazanar rusa yarjejeniyar kasuwanci tareda cire kasar Canada daga cikin jerin kasashen dake da hulda da kasar sa a kungiyar nan da aka yiwa sunan Alena.

Talla

Shugaba Trump ya bayyana cewa kasar ta Canada ta jima ta na morewa dangantakar dake tsakaninsu, ba tareda Amurka ta girbi wata riba a kai ba.

Bangaren hukumomin Canada, an dai bayyana cewa Firaministan kasar Justin Trudeau ya shiga tattaunawa da tsohon Firaministan kasar domin sanar da matsayar kasar sa dangane da wannan barazana ta Donald Trump.

A baya dai Shugaban na  Amurka Donald Trump ya sanar da cewar ya ribanya haraji akan karafa da kuma gorar ruwan dake zuwa daga kasashe irin su Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI