China- Afrika

China ta bai wa kasashen Afrika tallafin Dala biliyan 60

Shugaban kasar China Xi Jinping.
Shugaban kasar China Xi Jinping. REUTERS/Mike Hutchings

Shugaban China, Xi Jinping ya yi alkawarin bai wa kasashen Afrika tallafin Dala biliyan 60 don bunkasa yankinsu, yayin da ya shaida wa shugabanninsu cewa, babu wata manufa ta siyasa a game da jarin da kasarsa ke zubawa a nahiyar duk da caccakar da yake sha daga wasu bangarori.

Talla

Shugaba Jinping na magana ne gabanin bude taron kwanaki biyu tsakanin China da Afrika da ake saran zai mayar da hankali kan batutuwa da dama da suka hada da shirinsa na samar da hanyoyi da kayayyakin more rayuwa ta fuskar kasuwanci a kasashen ketare.

Manufar wannan shirin ita ce, inganta huldar kasuwanci tsakanin China da kasashen ketare, kuma tuni kasar ta bai wa wasu kasashe a yankin Asiya da Afrika rancen biliyoyin Dala don gina hanyoyin motoci da jiragen kasa da tashoshin jiragen ruwa da sauran manyan kayayyakin more rayuwa.

Sai dai wasu masharhanta da ke sukar shirinsa sun gargadi cewa, shugaban na kokarin binne wasu kasashen ne kawai ta hanyar tila musu tarin basuka.

Amma shugaban ya ce, ko kadan babu wata alamar siyasa a cikin shirin nasa, yayin da ya ce, kasarsa ba ta tsoma baki kan al’amuran cikin gida na kasashen Afrika.

Shugabannin Afrika da ke halartar taron sun hada da Muhammadu Buhari na Najeriya da Cyril Ramaphosa na Afrika ta Kudu da Abdel Fatah al-Sisi na Masar da Edgar Lungu na Zambia da kuma Ali Bongo na Gabon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.