Bakonmu a Yau

Garba Shehu kan taron China da Afrika a Beijing

Sauti 03:19
Shugaban China mai masaukin baki,  Xi Jinping
Shugaban China mai masaukin baki, Xi Jinping REUTERS/Damir Sagolj/File Photo

Shugabannin kasashen nahiyar Afrika na gudanar da taro na kwanaki biyu tare da shugaban kasar China Xi Jinping a birnin Beijing da niyyar raya nahiyar Afrika. Ministan Waje na  China Wang Yi, ya fada wa takwarorinsa cewa shugaba Jinping zai yi amfani da wannan dama domin gabatar da shirinsa na raya nahiyar. Garba Aliyu Zari ya zanta ta wayar tarho da mai magana da yawun  shugaba Muhammadu Buhari, wato Malam Garba Shehu daga China kan muhimmancin taron.