Venezuela

Hanyoyin magance kwararar jama'a daga Venezuela

Wasu yan kasar Venezuela dake kokarin tsallakawa zuwa Ecuador
Wasu yan kasar Venezuela dake kokarin tsallakawa zuwa Ecuador REUTERS/Daniel Tapia

Ministocin kasashen dake kudancin Amurka sun gudanar da wani taro a Quito domin samo hanyar magance matsalar bakin dake kwarara daga kasar Venezuela sakamakon cigaba da tabarbarewar al’amura a cikin kasar.

Talla

Ministocin daga kasashe 13 na bukatar neman agajin kudade domin kai dauki ga bakin dake cikin mawuyacin hali.

Taron na zuwa ne kafin wanda ake shirin gudanar a karkashin kungiyar kasashen Amurka a yau laraba wadda itama zata tattauna matsalar.

Gwamnatin Venezuela na zargin kasar Amurka da Majalisar Dinkin Duniya da kururuta ala’amarin domin samun damar kaiwa kasar hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.