Falasdinu-Isra'ila

Kotun Kolin Isra'ila ta bada izinin rusa kauyen Falasdinawa

Kotun Kolin Isra’ila ta bayar da izinin rusa wani kauyen Falasdinawa mai suna Khan El-Ahmar wanda ke karkashin mamayar kasar ta Isra’ila a gabar yamma ga kogin Jordan.

Falasdinawa na zanga-zanga a kusa da kauyen Khan el-Ahmar da kotu ta bada umarnin rusawa cikin mako guda
Falasdinawa na zanga-zanga a kusa da kauyen Khan el-Ahmar da kotu ta bada umarnin rusawa cikin mako guda ABBAS MOMANI / AFP
Talla

Mako daya bayan samun wannan izini, mahukuntan Isra’ila na iya rusa wannan gari, lamarin da zai iya kawo cikas ga yunkurin da bangarorin biyu ke yi domin samar da sulhu a tsakaninsu.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren sharhin da Dr. Yunusa Muhammad Sani na jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua ya yi kan lamarin a hirarsa da AbdoulKarim Ibrahim Shikal.

Dr. Yunusa Muhammad kan rusa kauyen Falasdinawa

A cewar Isra’ila, an gina wannan gari ba bisa ka’ida, yayin da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Turai da Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama suka nuna adawa da matakin rusa kauyen mai cike da gidajen katako da rumfunan wucen-gadi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI