Syria

Syria ta kaddamar da yaki a Idlib da nufin kawo karshen zaman yan tawaye

Fafatawa tsakanin dakarun gwamnatin Syria da yan tawaye a Idlib
Fafatawa tsakanin dakarun gwamnatin Syria da yan tawaye a Idlib Nazeer AL-KHATIB / AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci shugabannin kasashen Rasha da Turkiya su sanya hannu wajen hana Syria kaddamar da yaki a Idlib domin kaucewa kazamin zubda jinni a Yankin, bayan wani harin sojin Rasha da ya hallaka fararren hula 9.

Talla

Kiran Majalisar na zuwa a dai dai lokacin da wasu hare-haren sojin Rasha suka hallaka fararren hula 9 baya jikata wasu da dama a yankin na Idlib garin daya tilo da ya rage a hannun ‘yan tawayen kasar.

Jakadan Majalisar Dinkin duniya da ke kokarin sasanta rikicin Syria, Steffan de Mistura ya bukaci shugabannin biyu da su yiwa Allah su kira shugaba Bashar al Assad ta waya domin dakatar da kai hare haren ta sama.

Syrian dai ta sha alwashin kakkabe sauran ‘yan tawayen da suka rage a yankin na Idlib inda ta yi amfani da jiragen yakin Rasha wajen kai hare-haren ta sama.

Tuni dai Amurka ta yi gargadin cewa za ta dauki tsauraran matakai kan Syrian matukar ya tabbata cewa ta yi amfani da makamai masu guba kan mutanen ta.

A makon jiya ne dai dakarun sojin Syrian suka fara jibge tankunan yakin su gab da yankin na Idlib matakin da ke nuna cewa gwamnatin yria ta shirya domin hafkawa yan tawayen.

‘Yan tawayen da ke yankin na Idlib ko a makon jiya sun karya wasu manyan gadoji da suka hade yankin da yankunan da ke karkashin ikon gwamnati don hana dakarun shigowa bayan ganin wasu tarin tankunan yaki gab da yankin na Idlib.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI