Birtaniya-Rasha

Manyan kasashe sun goyi bayan Birtaniya a zargin Rasha da harin guba

Yanzu haka kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na can yana tafka mahawara kan rahotan.
Yanzu haka kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na can yana tafka mahawara kan rahotan. Matt Dunham/Pool via REUTERS

Shugabannin Kasashen Amurka da Faransa da Jamus da Canada sun bi sahun Birtaniya wajen goyan bayan binciken da aka gudanar da ke nuna cewar jami’an Rasha ne suka kai hari da makami mai guba London kan Sergei Skripal da ‘yar sa.

Talla

Shugabannin kasashen 5 sun bayyana cikakken goyan bayan su na cewar manyan jami’an gwamnatin Rasha ne suka ba da umurnin kai hari kan Skripal a wata sanarwar hadin gwuiwa da aka rabawa manema labarai.

Kasar Rasha ta yi watsi da zargin, inda ta ke cigaba da nesanta kanta da matakin.

Yanzu haka kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na can yana tafka mahawara kan rahotan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI