Faransa-Japan

Macron zai karbi bakoncin Yarima Naruhito na Japan

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. 路透社

Fadar Shugaban Faransa ta ce shugaba Emmanuel Macron zai karbi bakuncin Yarima mai jiran gadon Sarautar Japan, Naruhito ranar laraba mai zuwa a birnin Versailles, wanda zai kwashe mako guda yana ziyarar kasar domin karfafa dangantakar shekaru 160 da ke tsakanin kasashen biyu.

Talla

Ziyarar Yarimar wadda za ta fara daga gobe Juma’a a birnin Lyon, za ta mayar da hankali wajen tallata al’adun mutanen Japan, inda za’ayi bukukuwa da kuma bikin cin abinci.

Yarima Naruhito mai shekaru 58, shi ne babban dan Sarkin Sarakuna Akihito wanda zai zama Sarki na farko da zai sauka daga mukaminsa a watan Afrilun shekara mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI