Amurka-Trump

Manyan Jami'an Trump na zargin shi da kama karya

Kasidar wadda jaridar New York Times ta wallafa ta ruwaito wani babban kusa a gwamnatin ta Trump da ba a bayyana sunanshi ba na alakanta shuagban da mafi hadari ga kasar ta Amurka.
Kasidar wadda jaridar New York Times ta wallafa ta ruwaito wani babban kusa a gwamnatin ta Trump da ba a bayyana sunanshi ba na alakanta shuagban da mafi hadari ga kasar ta Amurka. REUTERS/Leah Millis

Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence tare da Sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo sun nesanta kan su daga wata kasida da Jaridar New York Times ta buga wadda ke bayani kan irin halin rudun dake cikin gwamnatin shugaba Donald Trump.

Talla

Kakakin mataimakin shugaban Jarrod Aggen ya ce babu gaskiyar cewar maigidansa ne ya rubuta kasidar, duk da ganowa wata kalma ta ‘lodestar’ a cikin ta da ake zargin cewar Pence na yawan amfani da ita.

Shima Mike Pompeo da ke ziyara yanzu haka a India, ya ce abin takaici ne a danganta shi da kasidar.

Ita dai kasidar da ba ta dauke da sunan kowa, ta bayyana shugaba Trump a matsayin mai hadari ga kasar ta Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.