Brazil

An daba wa dan takarar Brazil wuka a ciki

Jair Bolsonaro tare da magoya bayansa
Jair Bolsonaro tare da magoya bayansa Carl DE SOUZA / AFP

An kai hari da wuka  kan dan takarar jam’iyyar masu ra’ayi rikau a zaben shugabancin kasar Brazil da za a yi cikin watan gobe.

Talla

Jair Bolsonaro, an kai masa harin ne a ciki a lokacin da yake gabatar da jawabi ga magoya bayansa a wani taron gangami a kudancin kasar.

Tuni aka cafke wanda ake zargi da kai farmakin, yayin da aka yi wa dan takarar tiyata a hanjinsa kuma ana sa ran murmurewarsa.

Mr. Bolsonaro ya shahara da furta kalaman nuna kabilanci da kuma kyamatar masu luwadi da madigo, abin da ke bakantawa da dama daga cikin ‘yan kasar.

Kuri’un jin ra’ayin jama’a sun nuna cewa, Bolsonaro ka iya samun mafi yawan kuri’u a zaben shugabancin kasar muddin aka hana Luis Inacio Lula da Silva da ke kulle a gidan yari tsayawa takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.