Rasha-Syria-Turkiyya-Iran

Rasha ta yi luguden wuta ta sama a yankin Idlib na Syria

Jiragen yakin Rasha sun kaddamar da wasu tagwayen hare-hare ta sama kan yankin Idlib na Syria, Yanki daya kuma mafi girma da ya rage a hannun ‘yan tawayen kasar.

Matakin kai hare-haren yau asabar na zuwa ne bayan gaza cimma matsaya tsakanin kasashen da ke mara baya ga gwamnatin kasar da kuma masu mara baya ga 'yan tawayen na Syria.
Matakin kai hare-haren yau asabar na zuwa ne bayan gaza cimma matsaya tsakanin kasashen da ke mara baya ga gwamnatin kasar da kuma masu mara baya ga 'yan tawayen na Syria. OMAR HAJ KADOUR / AFP
Talla

Sabbin hare haren na zuwa ne kwana daya bayan Turkiyya mai goyon bayan ‘yan tawaye, da Rasha da Iran masu marawa gwamnatin Syria baya sun gaza cimma matsaya a Tehran kan hanyar da za a bi wajen kauce wa sabon rikicin a yankin na Idlib da ke yankin arewa maso yammacin Syria.

Jaridar Monitor ta ruwaito cewa, cikin kasa da sa’a 3 jirage kusan 60 ne suka yi luguden wuta a yankin da ke gab da kan iyakar Syria da Turkiyya, duk kuwa da bukatar dakatar da hare-haren da Majalisar Dinkin Duniya ta yi.

Kusan wata guda kenan jiragen Yakin na Rasha na kokarin kai farmaki yankin na Idlib don fatattakar sauran ‘yan tawayen da suka rage.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI