Rasha-Syria-Turkiyya-Iran

Taron birnin Tehran kan makkomar Idlib ya tashi baram-baram

Manzon MDD kan rikicin Syria, Staffan de Mistura, lokacin wani taro ranar 4 ga watan satumbar 2018 a New York.
Manzon MDD kan rikicin Syria, Staffan de Mistura, lokacin wani taro ranar 4 ga watan satumbar 2018 a New York. REUTERS/Denis Balibouse

Taron da shugabannin kasashen Rasha, Iran da kuma Turkiyya suka gudanar jiya juma’a domin fayyace makomar yankin Idlib wanda shi ne tungar karshe ta ‘yan tawayen Syria ya tashi baram-baram ba tare da cimma wata matsaya ba.

Talla

Da farko dai shugaba Racep Erdogan na Turkiyya ya bukaci Syria da kawayenta su amince da wani shirin tsagaita wuta domin kaucewa kai farmakin karshe a kan ‘yan tawaye da ke yankin, to sai dai shugaba Vladimir Putin ya ce ba ta yadda za a amince da wani shirin tsagaita wuta domin kuma ba wakilan ‘yan tawaye a taron na jiya.

Manzon musamman na MMD a game da rikicin Syria Staffan de Mistura, ya gabatar da wani shiri da ya tanadi janyewar ‘yan ta’adda da ke da nasaba da kungiyar Alqa’ida daga manyan birane da kuma yankunan fararen hula a lardin na Idlib, domin ganin cewa Syria da kawayenta ba su kaddamar da farmaki a kansu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.