Korea ta Arewa

Bikin cika shekaru 70 da kafa Koriya ta Arewa

Bikin cika shekaru 70 da kirkiro kasar Koriya a Arewa a birnin Pyongyang, 9 ga watan satamubar 2018
Bikin cika shekaru 70 da kirkiro kasar Koriya a Arewa a birnin Pyongyang, 9 ga watan satamubar 2018 Ed JONES / AFP

A wannan lahadi an gudanar da gagarumin faretin soji don murnar cika shekaru 70 da kafa kasar Koriya ta Arewa, to sai dai a wannan karo kasar ba ta fito da manyan makamanta na nukiliya da kuma wadanda ke cin dogon zango zuwa wata nahiya kamar yadda aka saba a lokacin gudanar da irin wannan biki ba.

Talla

Dubban sojoji ne suka yi faretin a gaban idon shugaba Kim Jong Un a birnin Pyongyang, yayin da manazarta ke cewa kin fito da manyan makaman cikin har da na nukiliya a wannan karo, alama ce ta mutunta yarjejeniyar farko ta sulhu da kasar ta kulla da Amurka.

A irin wannan biki ne dai Koriya ta Arewa ke yin amfani da ita domin yi wa Koriya ta Kudu da Amurka barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.