Syria-Rasha

Syria da Rasha na ci gaba da luguden wuta a yankin Idlib

Jiragen yakin Syria da na Rasha sun ci gaba da kai hare-hare ta sama kan yankunan Idlib da Hama yau Lahadi inda suka yi amfani da manyan bama-bamai ciki har da marasa linzami.

Hare-haren dai sun biyo bayan rashin cimma matsaya a zaman tattaunawar da ta gudana don samar da mafita ga rikicin na Syria a Tehran tsakanin kasashen Syria Rasha Turkiyya da kuma Iran.
Hare-haren dai sun biyo bayan rashin cimma matsaya a zaman tattaunawar da ta gudana don samar da mafita ga rikicin na Syria a Tehran tsakanin kasashen Syria Rasha Turkiyya da kuma Iran. REUTERS/ Bassam Khabieh
Talla

Rahotanni sun ce yankunan da hare-haren jiragen Syrian yafi shafa sun kunshi kauyukan Al-Habeet da Abdin dukkaninsu a kudancin yankin na Idlib mafi girma da ke hannun ‘yan tawayen kasar ta Syria.

Abangare guda ita kuma Rasha ta mayar da hankali wajen farmakar kauyukan Latamneh da Kafr Xeita dukkaninsu a arewacin yankin Hama.

Kafin yanzu dai sojin Syria sun musanta amfani da nau’ikan bama-baman marasa linzami saboda hadarin da su ke da shi amma daga bisani bayan wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar ta tabbatar da cewa suna amfani da nau’in bom din kan ‘yan tawayen kasar.

Hare-haren dai sun biyo bayan rashin cimma matsaya a zaman tattaunawar da ta gudana don samar da mafita ga rikicin na Syria a Tehran tsakanin kasashen Syria Rasha Turkiyya da kuma Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI