Amurka-ICC

Amurka ta yi barazanar daure alkalan kotun ICC

Bolton ya ce wasu daga cikin matakan da suke shirin dauka matukar kotun ta yi gigin tuhumar wani ba’amurke sun hada da hana alkalanta shiga kasar, sannan kuma ta rike kadarorinsu.
Bolton ya ce wasu daga cikin matakan da suke shirin dauka matukar kotun ta yi gigin tuhumar wani ba’amurke sun hada da hana alkalanta shiga kasar, sannan kuma ta rike kadarorinsu. REUTERS/Denis Balibouse

Amurka ta yi barazanar sanya wa kotun Kotun hukuntan manyan laifufuka da kuma cin zarafin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya takunkamai matukar dai kotun ta yi yunkurin hukunta dan kasar Amurka bisa zargin aikata laifufukan yaki a Afghanistan.

Talla

Mai bai wa shugaban kasar ta Amurka shawara kan sha’anin tsaro John Bolton, wanda ya sanar da wannan barazana, ya bayyana kotun da ke birnin Hague da cewa take-takenta na da hatsari kuma Amurka ba za ta amince da su ba.

Bolton ya ce wasu daga cikin matakan da suke shirin dauka matukar kotun ta yi gigin tuhumar wani ba’amurke sun hada da hana alkalanta shiga kasar, sannan kuma ta rike kadarorinsu kafin daga bisani a nemi bangaren shari’ar kasar domin bayar da izimin kwace dukiyoyin alkalan.

John Bolton wanda ke gabatar da jawabi a gaban kungiyar masu ra’ayin rikau ta Federalist Society, ya ce ‘’ta yaya kotun za ta fara tunanin hukunta Amurkawa alhakin kasar ba ta taba rattaba hannu domin amicewa da kafuwarta ba?’’ yana mai cewa hakan zai zama babban kuskure amma kuma mai hatsari ga kotun.

A cikin watan nuwambar shekarar bara ne babbar mai shigar da kara ta Kotun Fatou Bensouda, ta ce za ta bukaci alkalai su fara bincike kan zargin da ake yi wa Amurka na aikata laifufukan yaki a Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI