Amurka-Falasdinu

Amurka na barazanar kulle Ofishin jakadancin Falasdinu

Barazanar kulle Ofishin na zuwa ne kwanaki 2 gabanin bikin cika shekaru 25 da cimma yarjejeniyar birnin Oslo da ta amince da kafa kasashe Isra’ila da Falasdinu.
Barazanar kulle Ofishin na zuwa ne kwanaki 2 gabanin bikin cika shekaru 25 da cimma yarjejeniyar birnin Oslo da ta amince da kafa kasashe Isra’ila da Falasdinu. REUTERS/Kevin Lamarque

Amurka ta sanar da aniyar rufe Ofishin jakadancin yankin Falasdinu da ke birnin Washington a wani matakin baya-bayan nan da Donald Trump ke dauka don tilastawa shugabancin yankin mara baya ga shirin sasanta rikicin Gabas ta tsakiya.

Talla

Matakin na Trump wanda ke zuwa yau Litinin na da nufin tirsasawa shugabancin na Falasdinawa dawowa cikin tattaunawar sasanta rikicin gabas ta tsakiya wanda Falasdinun ta fice bayan da Trump ya tabbatar da bude Ofishin jakadancin Amurka a birnin Kudus.

Sai dai sanarwar da babban Sakataren Ofishin jakadancin na Faladinawa a Washington Saeb Erekat ya fitar ya matakin ya biyo bayan kokarin da shugabancin yankin ke yi wajen ganin kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta tuhumi Isra’ila da laifukan yaki.

Sanarwar ta Falasdinawa ta kuma bayyana matakin na Amurka da mafi munin hukunci da zai kara rura wutar rikicin yankin maimakon sasanta shi, haka zalika ba zai hana tuhumar da ake yiwa Isra’ila da keta hakkin bil’adama baya ga aikata laifukan yaki a yankin na Falasdinu ba.

Amurkan dai ta yi zargin cewa, shugabannin yankin na Falasdinu sun saba tsare-tsare da aka shirya na wanzar da zaman lafiya a yankin bayan da ta bukaci kotun ICC ta tuhumi wasu manyan jami’an Isra’ilan.

Barazanar kulle Ofishin na zuwa ne kwanaki 2 gabanin bikin cika shekaru 25 da cimma yarjejeniyar birnin Oslo da ta amince da kafa kasashe Isra’ila da Falasdinu.

Tun a watan Nuwamban bara Amurkan ta yi barazanar rufe Ofishin na PLO amma kuma ta dage yayinda ta gindaya sharadin sabunta rijistarsa duk bayan watanni 6 matukar Falasdinun na bukatar ci gaba da harkokinta a Washington.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI