Rasha

Rasha na gudanar da atisayen soji mafi girma

Atisayen sojin na bana shi ne mafi girma da Rasha ta gudanar tun bayan yakin cacar-baka
Atisayen sojin na bana shi ne mafi girma da Rasha ta gudanar tun bayan yakin cacar-baka (Photo : Reuters)

Kasar Rasha ta kaddamar da atisayen soji mafi girma da ya kunshi kimanin dakarun kasar dubu 300 a yankin gabashin Siberia.

Talla

Kasar China za ta tura dakarunta dubu 3 da 200 dauke da motoci masu silke da jiragen sama don shiga cikin atisayen mai taken Vostok-2018, yayin da Mongolia ita ma za ta tura nata dakarun.

Tun lokacin yakin cacar-baka a1981, raban da Rasha ta gudanar da gagarumin atisayen soji irin wannan duk da cewa, atisayen bana ya zarce na wancan lokacin wajen yawan dakaru.

Atisayen na bana na zuwa ne a dai dai lokacin da dangantaka tsakanin Rasha da Kungiyar Tsaro ta NATO ke dada tabarbarewa.

Dangantakar ta tabarbare ne sakamakon matakin da Rasha ta dauka na mamaye yankin Crimea na Ukraine a shekarar 2014.

Tuni NATO ta bayyana atisayen na Vostok 2018 a masayin shirye-shiryen wani babban rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.