Amurka

Shekaru 17 da harin September 11 a Amurka

Harin da Kungiyar Al Qaeda ta kai a ranar 11 ga watan Satumba ya hallaka mutane akalla dubu 3 a Amurka
Harin da Kungiyar Al Qaeda ta kai a ranar 11 ga watan Satumba ya hallaka mutane akalla dubu 3 a Amurka Sean Adair/Reuters

Shugaban Amurka Donaldo Trump na ziyara a jihar Pennsylvania don karrama fasinjojin da suka rasa rayukansu a jirgin saman United Flight 93 da ‘yan ta’adda suka karkata akalarsa don kaddamar da farmakin ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001, amma fasinjojin suka yi gwagwarmayar hana jirgin isa birnin Washington bayan sun fahimci manufar matukansa.

Talla

Jirgin na cikin jiragen sama hudu da mayakan kungiyar Al-Qaeda suka karkata akalarsu a wancan lokaci, yayin da ya yi hatsari a garin Shanksville mai tazarar kilomita 200 daga arewa maso yammacin birnin Washington.

Muradin mayakan shi ne amfani da jirgin wajen kai hari a babban birnin Amurka amma ya yi hatsari akan hanyarsa bayan fasinjojin sun yi kokarin karbe iko da tukin jirgin jim kadan da samun labarin manufar mayakan ta wayar tarho.

Ana kallon fasinjojin a matsayin jarumai, lura da rawar da suka taka wajen hana jirgin isa birnin Washington don kaddamar da hari, abin da ya tsirar da salwantar karin rayuka.

Makusantan fasinjojin ne suka sanar da su ta wayar salula cewa, tuni aka kai hari da jiragen fasinja guda biyu a Cibiyar Kasuwanci ta Duniya, don haka su yi taka-tsan-tsan.

An dai yi amanna cewa, maharan sun yi nufin amfani da jirgin ne wajen kai hari kan ginin Capitol, wato ginin da ke kunshe da Majalisun Dokokin Amurka da a wannan rana ke tsaka da gudanar da zamansu.

Shekaru 17 kenan da harin wanda ya lakume rayukan mutane kusan dubu 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI