EU

EU na bukatar karfafa alakarta da kasashen duniya

Shugaban gudanarwar Kungiyar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker.
Shugaban gudanarwar Kungiyar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker. REUTERS/Vincent Kessler

Shugaban Hukumar Gudanarwar Tarayyar Turai, Jean-Claude Junker ya bukaci kungiyar ta dauki matakan karfafa alakarta da kasashen duniya ta fuskar samar da kyawawan manufofi don bunkasa tattalin arzikinta a dai dai lokacin da yakin kasuwanci da ta’addanci da kuma fifita muradan kasa ke ci gaba da ta’azzara a sassan Duniya.

Talla

Juncker ya yin jawabinsa na shekara-shekara da ya gabatar gaban zaman Majalisar Kungiyar ta Tarayyar Turai a birnin Brussels ya bukaci EU ta yi tsayuwar-daka wajen ganin ta fuskanci kalubalen da ke gabanta musamman wajen magance matsaloli masu alaka da yakin kasuwanci.

A cewar Juncker dole ne EU ta kawar da duk wani yunkurin fifita muradun kasa fiye da na duniya wanda kai tsaye kalaman na Juncker ke caccakar matakan shugaba Donald Trump wanda ke fifita Amurka akan kowanne batu na maslahar duniya.

Juncker wanda ya ce, kasashen kungiyar 28 za su hadu tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar sabbin manufofin kungiyar ga kasashen duniya, don samar da mafita ga rikice-rikicen da sassan duniya ke fuskanta tun bayan takale-takalen Amurka na baya-bayan.

Shugaban hukumar ta Turai ya ce, tun bayan matakin Trump na ficewa daga yarjejeniyar  dumamar yanayi ta Paris da sanya manyan haraji ga kayakin da kasashen duniya ke shigarwa Amurka da ma ficewa daga yarjejeniyar Nukiliyar Iran wadanda suka janyo kace-nace a bangarorin kasuwanci da na tattalin arziki da kuma batutuwan masu alaka da musayar kudin kasashe, mataki ne da ke nuna cewa dole kungiyar ta EU ta mike tsaye tare da nuna matsayinta a duniya wajen magance matsalolin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.