Isra'ila

Natanyahu: Rufe ofishin jakadancin Falesdinu da Amrruka ta yi daidai ne

Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya bayyana farin cikin sa da matakin da Amurka ta dauka na rufe ofishin Jakadancin Falasdinu a Washington, wanda ya ce, matakan da suke dauka akan Yahudawa yayi hannun riga da na zaman lafiya.

Firaministan Israela  Benyamin Netanyahu a lokacin zaman taron majalisar ministocinsa a Jérusalem  29 yuli 2018.
Firaministan Israela Benyamin Netanyahu a lokacin zaman taron majalisar ministocinsa a Jérusalem 29 yuli 2018. Sebastian Scheiner /Pool via Reuters
Talla

A sanarwar da ya bayar, Netanyahu yace Amurka ta dauki matakin da ya dace kan rufe ofishin Jakadancin Falasdinu dake washigton.

Sanarwar ta kara a cewa, Israila na goyan bayan matakan Amurka ke dauka, kan ki shiga tattaunawar da Falasdinawa ke yi, haka kuma da yunkurin kaiwa kasar hari a hukumomin duniya wanda ba zai taba haifar da zaman lafiya ba.

Tattaunawar zaman lafiya tsakanin falestinawa da Izraela ta kara sukurkucewa ne, tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya bayan maida ofishin jakadancin Amruka a birnin kudus da ya bayana babban birnin kasar Izraila. Matakin da ya harzuka Falestinawan da ma sauran kasashen duniya, dake fatan ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI