Brazil

Lula, dake kurkuku ya janye daga takarar shugabncin Brazil

tsohon shugaban kasar Brazil Lula, a watan  maris 2018, inda yanzu haka ke kurkuku yana bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar
tsohon shugaban kasar Brazil Lula, a watan maris 2018, inda yanzu haka ke kurkuku yana bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar REUTERS/Rodolfo Buhrer

TSOHON Shugaban kasar Brazil Inacio Lula da Silva dake daure a gidan yari, ya janye shirin takarar san a sake neman shugabancin kasar kamar yadda hukumar zabe da kotu ta bada umurni, inda aka maye gurbin sa da mataimakin sa, Fernando haddad.

Talla

Wani taron shugabannin Jam’iyyar ma’aikatar kasar da aka gudanar a birnin Curitiba ya amince da sauya dan takarar kafin wa’adin da hukumar zabe gindaya ya cika.

Daruruwan magoya bayan sa suka taru a kofar gidan yarin da ake tsare da tsohon shugaban, yayin da mataimakin nasa ya karanta wasikar da Lula ya rubuta wadda ke tabbatar da shi a matsayin dan takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.