Duniya

Ana bukatar kudin yaki da cutuka a duniya

Cutukan Kanjamau da Tarin-Fuka na Cizon Sauro na ci gaba da kashe mutane a sassan duniya
Cutukan Kanjamau da Tarin-Fuka na Cizon Sauro na ci gaba da kashe mutane a sassan duniya FAROOQ NAEEM / AFP

Wata babbar gidauniyar agaji ta duniya ta bayyana cewar ana bukatar karin kudaden ci gaba da yakar cutukan kanjamau da tarin-fuka domin ganin kawo karshensu a duniya. Gidauniyar Global Fund ta ce, ta taimaka wa mutane sama da miliyan 17 da rabi ta hanyar ba su maganin da ke rage radadin cutar Kanjamau da kuma miliyan 5 da aka ba su maganin cutar Tarin-Fuka.

Talla

Global Funds ta yi gargadin cewa hatta damar da ake da ita tsawon lokaci ta yaki da cutar zazzabin cizon sauro na neman zama tarihi domin kuwa ana gab da rasa damar.

Babban daraktan Global Funds, Peter Sands ya ce dole ne a hada karfi da karfe wajen ceto al’ummar duniya daga hadarin cutuka irinsu HIV Aids, Tarin-Fuka da kuma Zazzabin Cizon Sauro.

A cewarsa ba a da fargabar gaza yakar cutar, domin kuwa matukar aka samar da kudaden da za a tallafa tare kuma da wayar da kan al’umma don bayar da hadin-kai, babu shakka wanzuwar nau’in cutukan 3 na gab da zama tarihi a duniya.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna yadda mutane miliyan 1 da dubu 800 suka kamu da cutar a HIV Aids a bara kadai, yayin da ake da mutane dubu 940 da suka mutu sanadiyyar cutukan biyu a sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.