Duniya-Ta'addanci

Kungiyoyin ta'addanci 120 ne ke kai hare-hare sassan duniya-rahoto

Cibiyar ta ce muddin masu fada aji ba su fuskanci irin wadanan kungiyoyi wajen sake musu tunani ba, za’a cigaba da fuskantar karuwar tashin hankali.
Cibiyar ta ce muddin masu fada aji ba su fuskanci irin wadanan kungiyoyi wajen sake musu tunani ba, za’a cigaba da fuskantar karuwar tashin hankali. AFP

Wani Rahoto da Cibiyar Tony Blair ta wallafa ya nuna cewa duk da nasarar da aka samu kan mayakan ISIS a kasashen Iraqi da Syria a cikin wannan shekara, yanzu haka akwai akalla wasu kungiyoyi 120 da ke cigaba da kai munanan hare hare a fadin duniya.

Talla

Rahoton wanda cibiyar ke fitarwa duk shekara ya ce, yanzu haka akwai kungiyoyin yan ta’adda 64 da ke wanzuwa a yankunan da ba su da nasaba da manyan tashe tashen hankulan da ake samu a duniya da suka hada da Afghanistan da Iraqi da Libya da Somalia da Syria da kuma Yemen.

Rahotan ya ci gaba da cewa banda wadannan manyan tashe tashen hankulan da ake samu, akwai wasu kungiyoyin da ke tada kayar baya a kasashen Masar da Mali da Najeriya da kuma Pakistan wadanda ke cikin jerin kasashe 10 da ke fama da munanan tashe tashen hankula.

Cibiyar ta ce muddin masu fada aji ba su fuskanci irin wadanan kungiyoyi wajen sake musu tunani ba, za’a cigaba da fuskantar karuwar tashin hankali.

Alkaluman da Cibiyar ta tattara sun nuna cewar, a shekarar 2017 an samu tashe tashen hankula sau 27,092 sakamakon hare haren wadannan kungiyoyi, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 84,023 daga kasashe 66 na duniya.

Alkaluman sun ce an samu munanan hare hare sau 7,841 akasashe 48, yayin da aka samu irin su 18 a kasashen da suka ci gaba.

Rahotan ya bayyana kungiyar Boko Haram a Najeriya da Jamaat Nasr al Islam ta Mali a matsayin wadanda suka fi kai munanan hare hare a Yankin Sahel da tafkin Chadi.

Cibiyar ta Tony Blair ta ce al’ummar Musulmi suka fi jikkata daga wadannan munanan hare haren da Yan ta’adda ke kai wa.

Rahotan ya ce har yanzu kasar Syria ce tafi fama da tashin hankali inda a bara aka kashe mutane 34,853.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.