Amurka

Mutane miliyan 10 na fuskantar barazanar guguwar Amurka

Hoton guguwar da aka dauka da tauraron dan Adam kafin isowarta Amurka kamar yadda ake tsammani
Hoton guguwar da aka dauka da tauraron dan Adam kafin isowarta Amurka kamar yadda ake tsammani NASA/Handout via REUTERS

Akalla mutane miliyan 10 a Amurka aka bayyana cewa, suna fuskantar barazanar guguwar Florence mai dauke da ruwan sama, in da hukumomi ke ta kira ga jama'a da su fice daga gidajensu kafin dirar guguwar mai gudun kilomita 175 cikin sa'a guda.

Talla

Jihohin dake fuskantar bala’in guguwar, sun hada da North Carolina da South Carolina da Virginia da kuma Georgia.

Shugaba Donald Trump yabi sahun gwamnoni da jami’an kula da agaji wajen kira ga mazauna yankunan da su kaucewa guguwar.

“Wannan babba ce, muna bukatar kare lafiyarku, ku kauce wa hanyar guguwar, ku saurari wakilan Yankunanku, South Carolina da North Carolina da Virginia, tana zuwa in da kuke, babu tabbacin za ta sauya hanya, zata zo nan bada dadewa ba, ku shirya kuma ina fatar Allah Ya kasance tare da ku.” In ji shugaba Trump.

Ana ganin guguwar wadda ake saran dirarta a ranar Alhamis, za ta haddasa ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama mai karfin gaske da take tafe da shi.

An yi hasashen cewa, ibtila’in guguwar zai haddasa asarar sama da Dala biliyan 170 tare da lalata gidaje akalla dubu 759.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.