Myanmar

Suu Kyi ta kare matakin garkame 'yan jaridar Reuters

Shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi.
Shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi. REUTERS/Kham/Pool

Shugabar Gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi ta kare matakin garkame ‘yan jaridar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters a gidan yari duk da caccakar da kasashen duniya ke yi kan matakin.

Talla

Suu Kyi ta ce, Wa Lone da Kyaw Soe Oo sun karya doka kuma hukuncin da aka yanke musu ba shi da alaka da keta ‘yancin fadin albarkacin baki.

An cafke ‘yan jaridar ne bayan sun mallaki wasu takarkdun izinin gudanar da bincike kan kisan da sojoji suka yi wa Musulman Rohingya.

Shugaba Suu Kyi na shan matsin lamba don ganin ta yi tsokaci kan rikicin Rohingya da kuma matakin na garkame ‘yan jaridar da aka yanke wa hukunci a farkon watan Satumba.

A wannan makon ne, Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Myanmar da kaddamar da yakin keta hakkokin ‘yan jarida.

Suu Kyi ta ce, an kulle ‘yan jaridar ne saboda laifin taka wata ayar dokar sirri amma ba wai don kasancewarsu ‘yan jarida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.