Amurka

Karfin guguwar Amurka ka iya raguwa- Masana

Ana sa ran guguwar ta haddasa ambaliyar ruwa mai yawa
Ana sa ran guguwar ta haddasa ambaliyar ruwa mai yawa NC/via REUTERS

Yayin da iska da ruwan sama suka fara isa jihar Carolina da ke gabashin Amurka, masana yanayi sun yi hasashen raguwar karfin guguwar da ake yi lakabi da suna Florence zuwa mataki na 1, to sai dai duk da haka mahukuntan kasar na a cikin shirin ko takwana kafin isar mahaukaciyar guguwar.

Talla

Da farko dai hasashen masana ya dora guguwar ta Florence ne a mataki na 4, lura da cewa har zuwa yammacin ranar Alhamis tana gudun kilomita 150 a kowace sa’a daya, to amma za ta iya rikidewa zuwa mataki na gaba a cewar hasashen masanan.

Tuni iska da kuma ruwan sama suka fara isa a jihar Carolina da ma wasu yankuna da ke gabar gabashin kasar ta Amurka, lamarin da kafin faruwarsa mahukunta suka bayar da umurnin kwashe mutane sama da milyan daya da dubu 700 domin nisantar da su daga yankin.

Hukumar Hasashen Yanayi ta Tarayya a Amurka, ta ce guguwar za ta iya mamaye yankuna da dama da ke gabashin kasar tare da yiyuwar kasancewar gidaje a cikin ruwan da zurfinsa zai kama daga mita biyu zuwa 2.7.

A bara warhaka an samu faruwar irin wannan guguwa da ke dauke da ruwan sama mai suna Maria, wadda alkaluma suka ce ta yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan dubu 3 a yankin Puerto Rico, shugaban Amurka Donald Trump ya musanta wadannan alkaluma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.