Syria

Mutane dubu 360 sun mutu a rikicin Syria na shekaru 7 - rahoto

Wani rahoton kungiyoyin da ke sanya idanu kan rikicin Syria ya nuna cewa akalla mutane dubu dari uku da sittin suka mutu cikin shekaru bakwai da aka shafe ana tafka rikici a kasar ta Syria, yayinda rahoton ke nuna cewa cikin ‘yan kwanaki baya-bayan nan ne adadin ya yi matukar karuwa.

Rahoton na nuni da cewa, akwai tarin fararen hula da yawansu ya kai dubu 110 da 687da suka mutu a rikicin ciki kuwa har da kananan yara fiye da dubu 20 sai kuma mata kusan dubu 13.
Rahoton na nuni da cewa, akwai tarin fararen hula da yawansu ya kai dubu 110 da 687da suka mutu a rikicin ciki kuwa har da kananan yara fiye da dubu 20 sai kuma mata kusan dubu 13. REUTERS/Omar Sanadiki
Talla

Rahoton na zuwa ne a dai dai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da jan kunne dakarun sojin Syria da na kawayenta game da zubar da jinin da za a iya fuskanta a hare-haren da su ke kaddamarwa a arewa maso yammacin Idlib yanki na karshe da ya rage a hannun ‘yan tawayen kasar.

Rahoton ya bayyana cewa cikin watanni shidan shekarar nan kadai an hallaka mutane fiye da 13 a kasar wanda suka kunshi mayakan ‘yan tawayen da kuma sojin gwamnati.

Ka zalika rahoton na nuni da cewa, akwai tarin fararen hula da yawansu ya kai dubu 110 da 687da suka mutu a rikicin ciki kuwa har da kananan yara fiye da dubu 20 sai kuma mata kusan dubu 13.

A cewar rahoton dai akwai ‘yan tawaye dubu 124 da suka mutu a yakin sai kuma kusan rabin adadin na sojin da ke yaki da su, da suka kunshi ko dai na Syrian ko na kawance ko kuma na sa kai masu biyayya ga Bashar alassad, ciki kuwa har da mayakan Hizbullah daga Lebanon su dubu daya da 665.

Haka zalika rahoton ya nuna yadda yakin ya lakume rayukan mayakan IS da na Alqaeda har dubu 64, sai kuma wasu dubu 64 mayakan sa kai na bangaren ‘yan tawaye ciki har da Kurdawa.

Rahoton ya ce akwai kuma wasu mutane su 250 da kawo yanzu ba a kai ga gano su waye ba da suma aka hallaka su a rikicin na Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI