Amurka

NASA ta aika da tauraron binciken dumamar yanayi

The ICESat-2 mission will measure the changing height of Earth’s glaciers, ice sheets and sea ice, one laser pulse at a time, 10,000 laster pulses per second.
The ICESat-2 mission will measure the changing height of Earth’s glaciers, ice sheets and sea ice, one laser pulse at a time, 10,000 laster pulses per second. ©Image credit: NASA

Hukumar binciken sararin samaniyar kasar Amruka (NASA) ta harba wani tauraron dan adam, dake kunshe da fitilar hasken Leser a sararin samaniya, irinsa na farko mafin inganci da ta aika a tashar bincikenta dake sararin samaniya.

Talla

Taurara 'ICESat-2, da aikin binciken da zai gudanar ya lakume dalar Amruka biliyan 1, zai dinga lura ne da yadda daskarariyar kankara ke ci gaba da narkewa ne a doron kasa sakamakon matsalar dumamar yanayi.

Tauraron dan adam din dake da nauyin rabin Ton, an harba shi ne a sasararin samaniya da misalin karfe 1h na ranar yau assabar agogon GMT 6h na safe a kasar Amurka, ta hanyar makalashi ga kurtun aika taurarin dan adam  Delta II,  daga sansanin Vandenberg na sojan Amruka dake jihar California.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.