Amurka

Mummunar Iska da ruwan sana ta kashe mutane 5 a Amurka

Mahaukaciyar iska da goguwa da ruwan saman nan da aka yi wa lakabi da Hurricane Florence ta dira a yankin Carolina inda ta fara barna tun yammacin Juma'a.

Hoton Guguwar Artuhur da ta shafi yankunan kasar Amurka da Canada
Hoton Guguwar Artuhur da ta shafi yankunan kasar Amurka da Canada REUTERS/NASA/Handout via Reuters
Talla

Mahaukaciyar goguwar ta fara ne da hallaka wata mace da yaron ta, kamar dai yadda ‘yan sanda suka karas.

Alkaluman mamata yau Asabar na nuna rayukan mutane biyar suka salwanta,

A cewar ‘yan sandan yankin Wilmington dake North Carolina inda ta fara dira  matar da jinjiranta itaciya dake kusa da gidansu ta afka masu suka mutu.

A yanzu haka  Shugaban Amurka Donald Trump ya ce a makon gobe ne zai yi tattaki zuwa yankin domin ganin irin barnar da mahaukaciyar goguwqar ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI