Syria

Ana zabukan Kananan Hukumomi a Syria

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad.
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad. Reuters

A kasar Syria, yau Lahadi ake zabukan kananan Hukumomi a  wuraren da ke hannun Gwamnati duk da cewa tun shekara ta 2011 ba’a yi irin wannan zabe ba saboda rashin zaman lafiya.

Talla

An bude tashoshin jefa kuriu tun da safe, kuma ana sa ran za su kasance a bude na tsawon sao'i 12.

Jimillan ‘yan takara  40,000 ke neman kujeru 18,478 a yankuna daban-daban da Dakarun kasar ke iko da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI