Amurka

Mahaukaciyar Goguwa Ta Kashe Mutane 13 A Amurka

Wani da motarsa ta makale cikin ruwa lokacin da iska da goguwar Florence ke barna
Wani da motarsa ta makale cikin ruwa lokacin da iska da goguwar Florence ke barna RFI

Rayukan mutane akalla 13 ake ganin sun salwanta sakamakon mahaukaciyar iska da goguwa da ruwan sama mai karfe da aka yiwa lakabi da Hurricane Florence data afkawa yankin kudu maso gabashin Amurka musamman yankin North Carolina.

Talla

Karfin gudun iska da goguwar ta ragu jiya Asabar, bayan barnan da ta yi a jihohi biyu.

Gwamnan North Carolina Roy Cooper ya fadawa manema labarai cewa suna sa ido sosai bayan wucewar bala'in, yayinda shi kuma Gwamnan South Carolina Henry MacMaster ke cewa yanzu an barsu da mummunar ambaliyar ruwa a yankin.

Yawancin wurare dai a jihohin biyu babu hasken wutan lantarki saboda abinda ya faru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.