Philippines

Mahaukaciyar Iska da ruwan sama ta kashe mutane 25 a Philippines

Mahaukaciyar iska da goguwan da ruwan saman  da aka yi wa lakabi da Super Typhoon Mangkhut wadda ta dira a kasar Philippines yammacin Jumaa,  yanzu haka ta zarce wasu wuraren bayan data kasha mutane biyu, da tilasta kwashe dubban mutane daga gidajensu.

Yadda jama'a a kasar Philippines ke fama da matsalar ambaliyar ruwa da aka samu
Yadda jama'a a kasar Philippines ke fama da matsalar ambaliyar ruwa da aka samu REUTERS/Erik De Castro
Talla

Wannan iska ana ganin tafi dukka na baya hadari da kasar ta fuskanta.

Mutane akalla miliyan hudu ake ganin sun shiga wani hali ya zuwa jiya Asabar da mahaukaciyar iskar ke barna, a tsubirin Luzon inda ta mamaye gidaje da gonaki.

Shugaban zaratan kai agaji  na kasar ya fadawa manema labarai cewa basu gama tantance irin barnar da tayi ba ya zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI