Syria

Isra'ila ta musanta hannu wajen kakkabo jirgin Rasha

Rundunar sojin Isra’ila ta jajanta mutuwar ilahirin fasinjojin jirgin yakin Rasha da sojin Syria suka harbo, a lokacin da jiragen yakinta suka kai hari kan wasu cibiyoyin sojin Syrian.

Daya daga cikin jiragen yakin Rasha
Daya daga cikin jiragen yakin Rasha AFP
Talla

Har ila yau Isra’ilar, ta dora alhakin aukuwar hadarin akan shugaban Syria Bashar al-Assad da kasar Iran.

Kalaman na Isra’ila sun zo ne jim kadan bayan zargin da Rasha ta yi mata, na yin amfani da jirgin yakinta a matsayin garkuwa a lokacin da ta kaddamar da wani farmaki akan wata cibiyar ajiyar makaman Syria da kawayenta.

Isra’ilar ta musanta zargin yin amfani da jirgin yakin na Rasha a matsayin garkuwa, domin a cewarta a lokacin da sojin Syria suka harba makaman kakkabo jiragenta, tuni sun dade da barin sararin samaniyar kasar ta Syria.

Wannan takaddama ta sanya a yau talata Rasha ta gayyaci jakadan Isra’ila da ke kasar, domin karin bayani kan zargin Isra’ilar da hannu wajen harbo jirgin yakin nata mai dauke da jami’ai 15.

A jiya Litinin ne dai sojin Syria suka yi kuskuren harbo jirgin yakin Rasha, sakamakon martanin da suka maidawa jiragen yajin Isra’ila, yayin farmakin da suka kai kan wata cibiyar ajiyar makaman kasar da ke garin Latakia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI