Rasha ta dora laifin mutuwar dakarunta kan Isra'ila
Wallafawa ranar:
Kasar Rasha ta dora wa Isra’ila laifin mutuwar jami’anta 15 bayan wani barin wuta a Syria ya kakkabo jirgin da ke dauke da su, yayin da Rashan ta yi barazanar daukan fansa.
Mai magana da yawun rundunar sojin Rasha, Ignor Konashenkov ya ce, sojin Isra’ila da ke kai hare-hare a Syria sun yi amfani da jirgin sojin Rasha a matsayin kariya, abin da ya sa wani harin dakarun Syria ya rutsa da su har lahira.
Konshenkov ya ce, jirgin Isra’ila samfurin F-16 ya kaddamar da wani farmaki a kusa da Latakia da misalin karfe 10 na dare kuma a dai dai lokacin da jirgin Rasha samfurin I1-20 ke dab da sauka.
Sai dai a dai dai wannan lokacin ne aka harbo makamin rokan da ya rutsa da jirgin na Rasha kamar yadda Konshenkoy ya yi karin bayani, kuma a cewarsa, suna da ‘yancin daukan matakin ramako kan Isra’ila.
Rasha ta ce, Isra’ila ba ta samu cikakken gargadin kaucewa yankin ba daga Isra'ila gababin farmakin.
Koda yake bayanai na nuna cewa, dakarun na Syria sun harbo jirgin Rashan ne cikin kuskure, abin da ake kallo a matsayin mafi munin al'amari da ya auku tsakanin kasashen biyu da ke kawance da juna a yakin Syria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu