Nijar

An sace jagoran Katolika daga Italiya a Nijar

Pier Luigi Maccalli dan kasar Italiya
Pier Luigi Maccalli dan kasar Italiya RFI hausa

An sace wani jagoran addinin Kirista dan kasar Italiya a yankin kudancin Jamhuriyar Nijar da ke kusa da kan iyaka da Burkina Faso.

Talla

Mai magana da yawun gwamnatin Nijar Abdourahamane Zakaria ya tabbatar da sace Pier Luigi Maccalli a cikn daren da ya gabata a gidansa da ke Bomoanaga.

Thomas Codjovi, jami’in Huldar Sadarwar Kungiyar Mishan mai yada akidar Katolika a Nijar, ya ce, wasu 'yan bindiga akan babura ne suka sace Macalli.

Codjovi ya ce, mutanen su takwas sun kutsa cikin gidansa tare da tilasta masa fitowa kafin daga bisani su yi harbin bindiga a sararin samaniya.

Nijar na fama da matsalar mayakan jihadi da ke sace-sacen mutane musamman a yankin kudu maso yammacin kasar.

Ko a cikin watan Afrilun da ya gabata, sai da aka sace wani Bajamushe da ke aikin bada agaji a kasar ta Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.