Rahoto

Ayyukan ta'addanci sun ragu a duniya

Mayakan ISIS
Mayakan ISIS AFP

Wani rahotan gwamnatin Amurka ya bayyana cewar, an samu raguwar ayyukan ta’addanci daga kungiyar IS a kasashen Syria da Iraqi saboda nasarar da aka samu a kansu, amma kuma hakan bai hana samun barazanar kai hare-hare a kasahsen duniya ba. Rahotan ya ce, kungiyar IS da Al-Qaeda da wasu masu tada kayar baya sun baza komarsu a sassan duniya wajen kaddamar da sabbin dabaru da amfani da makaman zamani.

Talla

Rahotan da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta rubuta ya ce, wadannan manyan kungiyoyin 'yan ta’addan da suka hada da IS da Al-Qaeda da makamantansu na ci gaba da samun fasahar amfani da makami mai guba da jiragen sama masu sarrafa kansu wadanda za su iya amfani da su domin kai harin nesa daga in da suke.

Rahotan gwamnatin na kan ayyukan ta’addanci na shekarar da ta gabata ya ce, kungiyoyin na amfani da kafar sadarwar intanet wajen jirkita fahimtar jama’a da kuma samun mabiya domin kai irin wadannan hare-hare.

Bugu da kari, rahotan ya ce, mutanen da suka tafi yaki kasashen Syria da Iraqi da Afghanistan suka kuma koma kasashensu na zama babbar barazana wajen kai munanan hare-hare a kasashensu.

Rahotan ya kuma ce, an samu raguwar hare-haren da ake kaiwa da kashi 27 a duniya da kuma raguwar kashe- kashen da ake samu da kashi 23 a shekarar 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.