China-Amurka

China ta musanta kokarin katsalandan a zaben Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na China Xi Jinping.
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na China Xi Jinping. Nicolas ASFOURI / AFP

Kasar China ta nesanta kanta daga zargin shugaba Donald Trump cewar, tana shirya yin katsalandan a zaben 'yan majalisun da za a gudanar a Amurka a cikin watan Nuwamba.

Talla

Mai Magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Geng Shuang ya ce, duk wanda ya san harkokin diflomasiyar China, ya san cewa ba ta katsalandan kan harkokin cikin gidan kasashen duniya.

Shuang ya ce, saboda haka ba sa bukatar ganin wata kasa ta yi katsalandan kan harkokin cikin gidanta.

Kakakin gwamnatin ya bukaci Amurka ta da ta rika mutunta 'yancin kasar.

Wannan na zuwa ne a yayin da kasashen biyu ke yakin kasuwanci a tsakaninsu, in da a baya-bayan shugaba Trump ya sanar da shirin sake lafta wa China haraji kan kayayyakin da kudinsu ya kai Dala biliyan 200, matakin da Chinan ta lashi takobin mayar da martani akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI