Faransa- Rasha- Janhuriyar Africa ta Tsakiya

Faransa Ta Goyi Bayan Tsarin Kungiyar Tarayar Africa Don Warware Rikicin Africa Ta Tsakiya

Dakarun Faransa Sangaris ke zagaye a yankin musulmi dake Bangui a watan biyu na shekara ta 2016.
Dakarun Faransa Sangaris ke zagaye a yankin musulmi dake Bangui a watan biyu na shekara ta 2016. rfi

Kasar Faransa ta ce tsarin da Kungiyar Tarayar Africa ta gabatar na warware rikicin kasar Janhuriyar Tsakiyar Afrika shine kawai hanya mafi dacewa da zai kai ga karshen tarzomar da ake samu a kasar

Talla

Wannan ya na nuna bata amince da tsarin da kasar Rasha ta gabatar ba don warware rikicin na Janhuriyar Tsakiyar Africa.

Ministan Waje na Faransa Jean-Yves Le Drian ya gabatar da matsayin Faransa a taron manema labarai a New York inda ake taron kasashen Majalisar Dinkin Duniya.

Matsayin Faransa na zuwa ne bayan da Rasha da Sudan suka yi taro a Khartoum karshen watan jiya inda suka gabatar da matsiyinsu don warware rikicin Janhuriyar Africa ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.