MDD

Hankula za su karkata kan Donald Trump a taron MDD

Shugaban Amurka Donald Trump na jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Amurka Donald Trump na jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Lucas Jackson

Shugabannin kasashe daga sassan duniya sun fara isa birnin New York, domin halartar babba taron zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 73. Akwai batutuwa da dama da taron zai tattauna a kai da suka hada da Koriya ta Arewa da kuma Iran, in da hankula za su karkata kan shugaba Donald Trump na Amurka wanda ke ci gaba da yamutsa harkar diflomasiyar duniya.

Talla

Bayan ya kawo karshen dambarwa tsakaninsa da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, sannan yasa kafa ya shure yarjejeniyar nukiliyar  Iran, shugaba Trump zai hau mumbari a ranar Talata a babban taron don fuskantar abokan gaba da kuma aminan da ba sa gamsuwa da  hulda da shi.

Kazalika a  karon farko  a ranar Laraba, Trump zai jagoranci taron Kwamitin Sulhu  na Majalisar kan dakile yawaitar makaman kare dangi da zai mayar da hankali kan Iran, wanda akwai yiwuwar zai janyo kace nace tsakanin manyan kasashen duniya.

Taron zai yi bita game da dawowar dangantaka mai armashi tsakanin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu da kuma irin nasarar da Amurka da Koriya ta Arewa suka samu wajen dakile barazanar nukilya da makamai masu linzami.

Duk a ranar Talatar, bayan shugaba Trump ya karkare jawabinsa, takwararsa na Iran Hassan Rouhani zai hau mumbari, in da zai mayar da hankali kan ummul’aba'isan shawarar Amurka ta yin watsi da yarjejeniyar nukiliyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.