Rasha- Syria

Rasha Za Ta Baiwa Syria Makaman Kakkabo Makamai

Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya shaidawa shugaba Bashar al Assad na Syria cewar kasar sa za ta sayar masa da na’urar kakkabo mamakai kirar  S-300 domin bunkasa tsaron ta.

Shugaban Rasha Vladimir Putin tare da shugaban Syrian Bashar al-Assad a wajen hutawa na  Sochi, Russia ranar 17 Mayu, 2018.
Shugaban Rasha Vladimir Putin tare da shugaban Syrian Bashar al-Assad a wajen hutawa na Sochi, Russia ranar 17 Mayu, 2018. REUTERS
Talla

Fadar shugaban Rasha tace shugaba Assad ya kira Putin ta waya, inda suka tattauna kan shirin samar da tsaro ga sojojin Rasha dake cikin Syria da kuma inganta tsaron sama na Syria baki daya.

Ministan tsaro na Rasha Sergei Shoigu ya ce shugaba Putin ya bada umurnin karfafa tsaro a cikin kasar ta Syria, kuma tuni aka horar da sojojin Syria kan yadda za su yi amfani da sabbin makaman da zasu samu.

A halin da ake ciki Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya gargadi Rasha game da saida makamai ga Syria gudun kada su fada hannuwan wasu 'yan taadda.

A cewar Netanyahu muddin sabbin makamai suka shiga hannuwan 'yan tawayen Syria za'a sami karuwar rashin zaman lafiya a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI