Amurka-China

Shugaban Amurka da na Koriya ta Arewa za su sake ganawa

Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un a Otel din Capella dake  Tsubirin Sentosa na Singapore a ranar 12 ga watan Yuni, 2018.
Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un a Otel din Capella dake Tsubirin Sentosa na Singapore a ranar 12 ga watan Yuni, 2018. rfi

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana niyyar sa ta sake ganawa da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un nan gaba saboda ya lura da irin nasarorin da aka samu bayan tattaunawar farko.

Talla

Shugaba Trump ya fadawa manema labarai a New York inda ake taron kasashen Majalisar Dinkin Duniya cewa da alamu lallai zai sake ganawa da shugaba Kim Jong Un nan bada dadewa ba.

Ya bayyana cewa “kamar yadda aka sani shugaban Korea ta Arewa ya rubuta kyakkyawar wasika inda yake neman a sake ganawa dashi zagaye na biyu” kuma za’a yi ganawar.

A watan shida na wannan shekara ne Shugabannin biyu suka gana a Singapore wanda shine karon farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI