MDD

Guteres: Rikice rikicen siyasa, tattalin ariki, da tsaro na ci gaba da raba kanun kasashen duniya.

sakataren Majailsar Dinkin Duniya Antonio Guterres na jawabin bude taron karo na 73
sakataren Majailsar Dinkin Duniya Antonio Guterres na jawabin bude taron karo na 73 Reuters

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bude taron kasashen duniya, tare da gargadin cewa karuwar sabanin Diflomasiyya tsakanin wasu kasashe na barazanar karya dokokin kasa da kasa, da kuma haddasa rashin zaman lafiya. Yanzu haka dai baya ga Antonio Guterres da ya gabatar da jawabin buda zaman taron, shugaban Amruka Donald Trump da na Fransa Emmanuel Macron sun gabatar da nasu jawaban.

Talla

Yayin gabatar da jawabinsa na bude taron zauren majalisar dinkin duniyar karo na 73 a yau Talata, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya koka kan karuwar takaddama tsakanin wasu manyan kasashen duniya, musamman ta fanonin tattalin arziki, siyasa da kuma tsaro.

Inda ya ce,” a halin da ake ciki kullum yarda raguwa take yi tsakanin al’ummomin kasashe da shugabanninsu, abin takaici a yayinda duniya ke dada dunkulewa, a lokaci guda kuma, ra’ayin fifita bukatun kai na yawaita. Kazalika, ana ci gaba da taka dokokin duniya, a dai dai lokacin da ake kokarin hadeta waje guda, a yayin da ake kuma ci gaba da samun rarrabuwar kanu a tsakanin al’ummomin duniya.”

Shugaban Amurka Donald Trump ne ya soma gabatar da jawabinsa bayan Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya, kuma kamar yadda aka za ta ya jaddada matsayinsa kan batun yarjejeniyar nukiliyar Iran.

“A watan da ya gabata muka maido da takunkuman da aka dagewa Iran bayan cimma yarjejeniyar Nukiliyarta a shekarar 2015, Karin takunkuman kan kasar za su soma aiki a farkon watan Nuwamba, haka kuma wasu zasu kara biyowa baya. Kuma muna aiki tare da kasashen da ke sayen danyen man Iran wajen ganin sun janye cinikinsu, domin ba z amu kyale kasar da ke goyon bayan ta’addanci ta mallaki makamai mafiya hadari a duniya nukiliya ba”.

A nasa bangaren shugaban Faransa Emmanuel Macron a lokacin da yake gabatar da nasa jawabin ya bukaci kasashen duniya da su kauracewa saka hannu kan yarjejeniyoyin kasuwanci da kasashen da suka fice daga yarjejeniyar dumamar yanayi ta birnin Paris, ba tare da ya ambaci sunan Amruka ba, wace ta fice daga yarjejeniyar a 2017

Sauran manyan batututwan da ake sa ran taron shugabannin kasashen na duniyar zai tattauna a kai, sun hada ne da yakin Syria, ‘yan gudun hijirar Myanmar da kuma batun rage dumamar yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.