Faransa-Amurka

An yi ganawa tsakanin shugaban Fransa da na Amruka a birnin New York

shugaba Macron da Trump, sun gana a daura da taron MDD a birnin New York a ranar  24 satumba 2018
shugaba Macron da Trump, sun gana a daura da taron MDD a birnin New York a ranar 24 satumba 2018 REUTERS/Carlos Barria

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gana da takwaransa na Amurka, Donald Trump a birnin New York, gabanin soma taron koli na Majalisar Dinkin Duniya. Inda suka tattauna batun banbance-banbance da ke tsakanin kasashen biyu. A cewar sanarwa daga Fadar Elysee, Ganawar da ta dau tsawon sa’o’i hudu, anyi ta a Otel Manhatan, inda shugabannin biyu suka tattauna manyan batutuwan duniya, ciki har da batun Syria, da Iran da kuma jayeyyar cinikayya.

Talla

Shugaban Amurka Donalt Trump, ya bayyana ganawar, ta yi nasara duk da cewar akwai dan ban-bancin ra’ayi kan wasu batuwa tsakanin su.

Ana shi bangaren shugaban Faransa Emanuel Macron ya ce, bukatan wannan tattaunawar dai ta haifar da sakamako mai kyawu, masamman muradun kasashen biyu, da suka hada da yaki da ta’addanci da butun Gabas ta tsakiya.

An dai yi ganawar ce, gaban mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence da wasu Jakadu, inda shugabannin biyu suka yi musabaya har sau biyu gaban kamarori, to sai dai ga dukkan alamu ganawar bata yi armashi sosai ba kamar ganawar su ta farko.

Kuma a yau dinnan shugabanin biyu, Emanuel Macron da Donalt Trump suka gabatar da jawabai a zauren Majalisar Dinkin Duniya, wanda shugannin kasahe 130 ke halarta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI