Amurka-MDD

Ba za mu bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba-Trump

Shugaban Amurka  Donald Trump a yayin jagorantar taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York
Shugaban Amurka Donald Trump a yayin jagorantar taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York REUTERS/Eduardo Munoz

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakan da suka dace wajen hukunta kasashen da ke amfani da makamai masu guba. A yayin gabatar da jawabin bude taron Kwamitin Sulhu na musamman kan yaki da makamai masu guba, shugaban ya ce, ba za su bari kasar Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.

Talla

Shugaba Trump da ya zama shugaba na farko da ya jagoranci taron Kwamitin Sulhun, ya jaddada matsayin kasarsa na mallaka da kuma amfani da makamai masu guba.

Trump ya ce, "Kasashen duniya sun dade da gano cewar wasu makamai na da matukar hadari, kuma suna iya haifar da matsala sosai, wanda hakan ya sa daukacinmu ke da aniyar hana ci gaba da sarrafa su da yada su da kuma amfani da su."

"Daya daga cikinmu sun mayar da hankali kan hadarin da ke tattare da makamin nukiliya, amma kuma bai dace mu manta da hadarin da ke tattare da makamai masu guba ba. Tun bayan yakin duniya, mun jagoranci yunkurin kasashen duniya, domin dakile yaduwar yaki da makami mai guba" In ji Trump.

Shugaban ya kara da cewa, 'Nan bada dadewa ba mun dauki matakai masu tsauri kan Syria har sau biyu kan gwamnatin Assad saboda amfani da makami mai guba kan fararen hular kasar da basu ji basu gani ba."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.