Birnin Kudus ba na sayarwa bane - Abbas

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas yayin gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya da ke karbar bakuncin taron shugabannin kasashen duniya karo 73. 27 ga watan Agusta, 2018.
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas yayin gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya da ke karbar bakuncin taron shugabannin kasashen duniya karo 73. 27 ga watan Agusta, 2018. REUTERS/Carlo Allegri

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yayi amfani da kakkausan harshe wajen sukar Isra’ila da Amurka, dangane da matsayinsu kan rikice-rikicen yankin Gabas ta Tsakiya, yayin jawabin da ya gabatar a zauren majalisar dinkin duniya.

Talla

Kalaman farko da Abbas yayi amfani da su wajen bude jawabin nasa sune “Birnin Kudus bana sayarwa bane”, kalaman da suka haddasa barkewar tafi a zauren majalisar dinkin duniyar ga shugaban na Falasdinawa.

Shugaban Falasdinawan ya soki Isra’ila, bisa matsayin da take kai dangane da al’amuran yankin Gabas ta Tsakiya, musamman kan dokar da ta kafa ta mayarda ita kasar Yahudawa zalla.

Abbas ya ce kafa kasar Yahuduwa zalla tamkar rusa shirin ware-ware rikicin Falasdinu da Isra’ilar ce, ta hanyar amincewa da kafuwar kasar Falasdinu, matakin da ya ce Amurka na goyon bayansa ido rufe.

A jawabinsa na farko ga zauren majalisar dinkin duniya tun bayan sauya hedikwatar Isra’ila daga Tel Aviv zuwa Birnin Kudus, Mahmoud Abbas, ya ce Falasdinawa a halin yanzu suna kallon Amurka ne a matsayin mara adalci a shiga tsakanin da take yin a sulhunta rikicin Isra’ila da Falasdinu.

Shugaban Falasdinawan ya kuma soki Amurka dangane da matakin da ta dauka na janye tallafin dala miliyan $300 da take baiwa hukumar UNRWA ta majalisar dinkin duniya da ke kula da Falasdinawa ‘yan gudun hijira akalla miliyan 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.