Amurka-Canada-Mexico

Hannayen jari sun tashi saboda yarjejeniyar Amurka

Tutocin kasashen Mexico da Canada da Amurka
Tutocin kasashen Mexico da Canada da Amurka Lars Hagberg / AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana yarjejeniyar kasuwancin da suka cimma da kasashen Canada da Mexico a matsayin gagaruma. Tuni kasuwannin hannayen jari na kasashen duniya suka tashi a ranar Litinin biyo bayan wannan yarjejeniyar mai cike da tarihi tsakanin kasashen uku.

Talla

Kasashen Amurka da Canada da Mexico sun cimma sabuwar yarjejeniyar ce wadda ta maye gurbin tsohuwar yarjejeniyar kasuwancin bai-daya a yankin arewacin Amurka a daren da ya gabata.

A wani sakon Twitter da ya fitar, shugaba Trump ya ce, yarjejeniyar gagaruma ce ga dakkanin kasashen kuma za ta samar da mafita game da matsalolin da waccan tsohuwar yarjejeniyar ta fuskanta.

A cewar Trump, sabuwar yarjejeniyar ta USMCA, za ta bai wa manoma da masu samar da kayyaki wata damar a dama da su kasuwanni, sannan kuma za ta takaita shingen kasuwanci a Amurka tare kuma da hada kan kasashen uku don gogayya da sauran kasashen duniya.

Tuni masharhanta suka fara fashin baki kan wannan yarjejeniya, in da wasu ke cewa, za ta inganta wa manoman Amurka hanyoyin shiga kasuwannin madarar shanu ta Canada.

Bayan cimma yarjejeniyar, shi ma shugaban Canada, Justin Trudeau ya ce, wannan rana ce mai kyau ga kasarsa, yayin da shi ma Ministan Harkokin Wajen Mexico, Luis Videgaray ya yi madalla da ita.

A can baya dai, Mr. Tump ya sha caccakar tsohuwar yarjejeniyar kasuwancin ta bai-daya, in da har ma ya yi barazanar soke ta baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.