Rasha- Netherlands

Rasha ta kai harin Intanet a Netherlands

Rasha ta musanta kaddamar da harin intanet a kowacce kasa
Rasha ta musanta kaddamar da harin intanet a kowacce kasa Reuters/Kacper Pempel/Files

Hukumomin Tsaron Netherlands sun ce, sun dakile wani harin intanet da Rasha ta kai wa shafin hukumar da ke sa ido kan makamashin nukiliya ta duniya.

Talla

Ko a watan Afrilun da ya gabata, sai da Netherlands ta kori wasu da ake zargin ‘yan leken asirin Rasha ne, a wani yunkurin da ake ganin hukumar leken asirin sojin Rasha ke yi na yi wa hukumar rage yaduwar makamai masu guba ta duniya kutse a birnin Hague.

A wannan karon, Netherlands ta yi zargin cewa, Rasha ta makare wata mota da kayayyakin komfuta a wajen ajiyar motoci na wani otel, kusa da ofishin hukumar yaki da yaduwar makamai masu guba, in da ta yi kokarin kutsawa cikin rumbun bayananta.

Tuni gwamnatin Netherlands ta ce, ta gayyaci jakadan Rasha a kasarta don ya amsa wasu tambayoyi, bayan shugaban hukumar leken asirin na Netherlands, Manjo Janar Onno Fichelshiem ya nuna wasu fasfo-fasfo da ke tabbatar da cewa wadanda ake zargin ‘yan Rasha ne.

Ita ma Canada ta ce, ta fuskanci wannan hari daga Rasha a hukumar yaki da shan kwayoyi masu kara kuzari tsakanin ‘yan wasan motsa jiki da ke Montreal.

Ita ma Amurka ta fito ta zargi wasu jami’an leken asirin Rasha 7 da ke da nasaba da korafin da Nehterlands ta yi, in da har sakataren tsaron Amurkan James Mattis ya ce, kasarsa za ta bai wa kungiyar  tsaro ta NATO gudummawar makamanta na yaki da harin intanet don dakile Rasha.

Har yanzu dai Rasha ta ci gaba musanta wannan zargi da kasashen duniya da kungiyoyi ke yi mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.