Indonesia

Har yanzu babu labarin mutane dubu 1 a Indonesia

Babu duriyar sama da mutane dubu 1 a Indonesia bayan aukuwar girgizar kasa a makon jiya.
Babu duriyar sama da mutane dubu 1 a Indonesia bayan aukuwar girgizar kasa a makon jiya. REUTERS/Athit Perawongmetha

Mako guda bayan ibtila’in girgizar kasa a Indonesia, mutane sama da dubu daya har yanzu babu duriyarsu, yayin da yawan mamata da aka samu gawarwakinsu suka kai  dubu 1 da 571.

Talla

Ya zuwa yanzu, birnin Palu da ke tsibirin Sulawesi ya zama kufai, bayan girgizar kasa da ambaliyar ruwa da aka samu da suka mamaye garin.

Ana fargabar cewa, akwai mutane masu yawan gaske da kasa ta binne su, musamman mazauna rukunin wasu gidaje da ke Balaroa in da girgizar kasar tafi muni.

Bayan kusan mako daya da aukuwar girgizar kasar , yanzu haka tallafi na isa ga mabukata daga sassan duniya, yayin da kidddigar Majalisar Dinkin Duniya ke cewa akalla mutane dubu 200 ne cikin bukatar agajin gaggawa a kasar.

Mutane da yawa da suka tsira da rai daga girgizar kasar na ci gaba da yawon neman abinci da wasu muhimman bukatu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.