Isa ga babban shafi
Amurka

Majalisar Amurka ta amince da Kavanaugh a matsayin alkali

Brett Kavanaugh
Brett Kavanaugh 路透社
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Majalisar Dattawan Amurka ta amince da nadin alkali Brett Kavanaugh a matsayin alkalin kotun koli duk da zarge-zargen da aka masa na cin zarafin mata da kuma lalata da su bayan ya dirka musu giya.

Talla

'Yan majalisu 51 suka kada kuri’ar amincewa da nadin, yayin da 49 suka ki, cikin su har da Sanata Lisa Murkowski, Dan Jam’iyyar Republican da ya bijire wa matsayin Jam’iyyarsa.

A ranar Asabar ake saran kada kuri’a ta karshe, sai dai wata 'yar majalisar daga Jam’iyyar Republican Susan Collins ta ce, tana tababa wajen hukuncin da za ta yanke.

Tuni shugaba Donald Trump ya bayyana farin cikinsa da nasarar da ya samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.